<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>454</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 KORUS
 Ku yi sowa farin ciki, duniya duka
 Ga Ubangiji gama nagari ne shi.

[V2]
 1) Ku yi masa bauta da farin zuciya
 Ku zo gabansa da rerawa
 Ku sani Ubangiji shi ne Allah.
 Shi ne yayi mu.
 Korus

[V3]
 2) Ku sani Ubangiji ne ya yi mu
 Ba mu ne muka yi kanmu ba
 Mu ne mutanensa
 Tumakin makiyaya tasa.
 Korus

[V4]
 3) Ku shigo ƙofofinsa da godiya
 Cikin harabunsa da rerawa
 Ku yi masa godiya
 Ku albarkaci sunansa
 Korus

[V5]
 4) Gama Ubangiji nagari ne shi
 Jinkansa madawami ne
 Amincinsa ya tabbata
 Daga tsara zuwa tsararaki.
 Korus</lyrics>
<title>Ku Yi Sowa Farin Ciki LW454</title>
</song>